WikiFX APP

Global Forex Broker Regulatory Inquiry APP

Download

Menene Forex (canjin kudade)?

WikiFX   |   2021-12-27 15:21:31

  A saukake ma’anar sa ita ce kasuwar cinikayya ta duniya wadda take bada dama ayi kasuwancin kudade.

  Idan kana tunanin kudin kasa daya zaifi na wata kasar daraja, kuma hasashenka yazama gaskiya, to zaka iya samun riba.

  A wani lokaci daya shude, kafin zuwan annobar data gallabi duniya, mutane suna iya shiga jirgin sama suyi tafiya kasa kasa.

  Idan ka taba yin tafiya zuwa wata kasar, zai zama sai ka nemi wajen canjin kudi a filin tashin jirgin sama, domin ka canja kudin dakake dashi a jakarka/aljihunka zuwa kudin kasar da zaka kai ziyara.

makaranta

  Zakaje wajen canjin, a sama zakaga allo yana nuni da farashin canji na kudade daban daban.

  Farashin Canji: shi ne kiyasin farashin kudade guda biyu na kasashe guda biyu mabanbanta.

  Zakaga kudin Japan kayi murna kace ‘’dala ta guda daya daidai take da yen din Japan guda dari? Gashi kuma inada dala goma, nayi arziki. Kanayin haka kayi kasuwanci a kasuwar canjin kudi (Forex).

  Ka canja kudi daya zuwa wani kudin daban.

  Ko idan a bangaren kasuwar canjine (Forex), misali kai dan Amurka ne zaka kai ziyara Japan, sai ace ka siyar da daloli ka sayi yen.

makaranta

  Kafin ka dawo gida, zaka sake tsayawa awajen canji na filin jirgin sama domin ka canja ragowar yen din dakayi sa’a ya rage maka. (Domin Tokyo garine mai tsadar rayuwa!) sai ka kula dacewa farashin canjin ya canja.

  Wadannan canje canjen na farashin kudi, su suke bawa mutum dama ya samu kudi a kasuwar canjin kudi.

  Menene Canjin Kudi (Forex)?

  Kasuwar canjin kudi, wacce akafi sani da kasuwar canji wato “forex” ko ‘’FX’’ ita ce kasuwar cinikayyar kudi mafi girma a duniya.

  Kasuwar cinikayyar kudi kasuwa ce ta duniya, wadda bata karkashin ikon kowa, kasuwa ce da ake canjin kudaden duniya acikinta. Farashin canji yana canjawa a kasa da kowacce dakika. Saboda haka kasuwar koda yaushe acikin canjawa take.

  Dan kankanin kaso cikin hadahadar kudine kawai yake faruwa a kasuwa ta zahiri wadda ta kunshi kasuwancin kasa kasa dakuma yawon bude ido kamar misalign daya gabata na filin jirgin sama.

  Saidai, mafi yawancin hadahadar kudin da take wakana a kasuwar canji ta duniya ana siyo sune (a kuma siyar) saboda wasu dalilai na samun riba mai yawa ko akasin haka.

  Yan kasuwar canji suna siyan kuddade da saran cewa zasu siyar dasu da tsada a nan gaba.

  Idan aka kwatanta kankanin kudi $22.4 billion a ma’aunin kowacce rana na kasuwar cinikayyar kayayyaki ta New York (NYSE), kasuwar canji kasuwace mai girman gaske wadda ma’auninta na kowacce rana yakai kimanin $6.6 TRILLION.

  Bara mudauki dan lokaci muyi amfani da dodanni wajen misalin wannan bayanin.

  Mafi girman Kasuwar cinikayyar kayayyaki a duniya ita ce kasuwar cinikayyar kayayyaki ta new York (NYSE), wadda take kasuwancin misalin $22.4 billion a ma’aunin kowacce rana. Idan mukayi amfani da dodo wajen misalta NYSE. Misalin zai zama kamar haka…….

makaranta

  Yayi kama da abun ban haushi. Kamar yayi atisaye. Wasu zasu iya cewa yayi kyau.

  Kullum a labarai zaku dinga jin labarai akan NYSE…..a tashoshi kamarsu CNBC… a Bloomberg… a BBC…. watakila ma kaji labarin a gidan atisayen ku. NYSE tayi sama, ta kara daraja da sauransu.

  Idan kaji mutane suna Magana akan “kasuwa”, mafi akasari suna magane ne akan kasuwar kayayyaki. Hakan yasaka labarin NYSE ya shahara acikin mutane, ake yawan jin duriyarsa.

  Amma idan zaka kwatanta shi da kasuwar canjin kudi, to zaiyi kama da haka….

makaranta

  Tofa, NYSE dan kankanin abu ne idan aka kwatantashi da kasuwar canjin kudi! Bama za’a taba hadawa ba.

  Kuyi duba da jadawalin ma’aunin kasuwar canji a kowacce rana, New York Stock Exchange, Tokyo Stock Exchange, dakuma London Stock

Exchange:

makaranta

  Kasuwar kudade ta ninka kasuwar kayayyaki sau 200. Tanada girman gaske.

  Amma ku saurara akwai bayani!

  Wannan adadi mai girman gaske da yakai dala $6.6 trillion shi ne ya mamaye gaba daya kasuwar canji ta duniya, amma kuma ita kasuwar “spot”, wadda ita ce bangaren kasuwar kudi da take da muhimmanci ga mafi yawancin yan kasuwar canji, yar karama ce wadda ma’auninta yakai kimanin dala $2 trillion a kowacce rana.

  Sannan, idan anada bukatar kirga adadin kasuwancin kudi daga yan kasuwar sodore (mukenan), to adadin yafi haka karanci.

  Abune mai wahalar gaske asan hakikanin girman bangaren kasuwancin sodore na kasuwar canji, amma an kiyasta cewa zaikai wajen kaso 3-5% nagaba daya kasuwancin canji a kowacce rana, ko kuma zaikai wajen dala $200-300 billlion (watakila kasa da haka).

  Wannan yana nuni da cewa kasuwar canji kasuwa ce mai girman gaske, ba kamar yadda wasu sukaki yadda da girmanta ba.

  Kar ku yarda cewa “kasuwar canji takai dala $6.6 trillion” kambabawa ce! Adadin yanada sha’awar gani amma yanada yar yaudara aciki. Bamason kambaba abu. Munfison fadin gaskiya.

makaranta

  Bayan girman kasuwar canji, kasuwar da wuya ta rufe! A bude take akoda yaushe.

  Kasuwar canji a bude take tsawon awa 24 a kowacce rana har tsawon kwana biyar (5) a kowanne sati. Ana rufeta ne kawai akarshen sati.

  Saboda haka, ba kamar kasuwancin kayayyaki ba ko sauran kasuwanci, kasuwar canji BATA rufewa a karshen kowacce ranar kasuwa.

  Saidai, kasuwancin yana matsawa ne zuwa wasu cibiyoyin na duniya.

makaranta

  Rana tana farawa a sanda dan kasuwa ya wayi gari a garin Auckland/Wellington, sannan ta matsa zuwa garin Sydney, Singapore, Hong kong, Tokyo, Frankfurt, London, sannan daga karshe New York, kafin daganan cinikayya ta sake farawa daga farko a garin New Zealand.

  Domin taimakawa wajen sanin abunda yake faruwa a kasuwar canji a kowacc rana, mun samar da manhajar kasuwancin canji. Manhaja ce da take nuni akan takaitattun bayanai akan halin da kasuwar canji take ciki a yanzu, wannan yana bawa yan kasuwa dama susan halin da kasuwa take ciki cikin gaggawa, sannan su fahimci wasu manyan kudade ne suke da karfi ko kuma rashin tabbas, sannan wasu jerin kudade biyu ne sukafi samun riba ko sukafi faduwa.

  A sashe nagaba, zamu bayyana cikakken abunda ake cinikayya dashi a kasuwar canji

Kara